Ba za mu gama aiki kan kasafin 2025 ba kafin sabuwar shekara – Majalisar Dattawan Najeriya

Spread the love

Majalisar Dattawan Najeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar da kada su tsammaci za ta kammala tantance kasafin kuɗin 2025 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gabatar mata kafin sabuwar shekara.

A ranar 18 ga watan Disamba ne Tinubu ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 49.7 a zaman haɗin gwiwa tsakanin ‘yanmajalisar dattawa da na wakilai, kuma ya neme su da su gaggauta amincewa da dokar.

Shugaban kwamatin yaɗa labarai na majalisar, Sanata Yemi Adaramodu (APC a jihar Ekiti) ya faɗa wa manema labarai jiya Lahadi cewa sai a ranar 7 ga watan Janairu ma za su fara sauraron jawabin kare kasafi na hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Ya ƙara da cewa kwamatin kula da harkokin kuɗi na majalisun zai gabatar da rahotonsa na ƙarshe ne a ranar 31 ga watan na Janairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *