Ba za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi ba a jihar Jigawa – PDP

Spread the love

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ba za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a jihar ba.

PDP ta cimma matsayar ƙin shiga zaɓen ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, a cewar wata sanarwa daga shugaban jam’iyyar, Alhaji Aliyu Idris Diginza.

Cikin sanarwar, PDP ta zayyana dalilanta na fasa shiga zaɓen da za a yi a ranar 5 ga watan Oktoba. Wasu daga cikin dalilan sun haɗar da:

  • Rashin tsammanin adalci daga hukumar zaɓen jihar ta Jigawa mai suna SIEC.
  • Babu isasshen lokaci da aka ba wa jam’iyyun adawa domin su yi shirin shiga zaɓe.
  • An tsawwala kuɗaɗen sayen fom na shiga takara domin a hana ‘yan jam’iyyun adawa damar saye da kuma shiga zaɓe.
  • Akwai yiwuwar ba wa ‘yan jamiyyar APC da wasu ƙananan jam’iyyu kyautar fom ɗin tsayawa takara.

Sanarwar ta ce: “PDP ta yi lissafi cewa Idan za ta sayi fom ɗin takara sai ta kashe naira miliyan 709, idan kuma jam’iyyu 10 za su sayi fom hukumar zabe ta jihar, SIEC, za ta karɓi kuɗin da ya zarta naira biliyan bakwai, wanda hakan ya wuce adadin kasafin kuɗin da doka ta amince su kashe ganin cewa hukumar SIEC ba kamfanin cin riba ba ce.”

PDP na da Sanata guda, da ‘yanmajalisar tarayya biyu, da na jiha ɗaya a jihar ta Jigawa, wadda APC mai mulkin Najeriya ke jagoranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *