Ba zan ce uffan ba kan dambarwar da ke faruwa a jam’iyyar NNPP ba – Kwankwaso

Spread the love

Ɗantakarar shugabancin ƙasar Najeriya, a jam’iyyar NNPP kuma jagoran kungiyar Kwankwasiyya , Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ba zai magana dangane da dambarwar da ke cikin jam’iyyar tasu a Kano ba.

Kwankwaso wanda ya shaida wa ƴan jarida hakan bayan wani taron karɓar ƴan jam’iyyar APC da suka sauya sheƙa zuwa NNPP a gidansa da ke birnin kano, ya ce “ba na son na tattauna a kan wannan batun. Ka da ku tsoma ni a cikin al’amarin da bai kamata na shiga ciki ba. Shugaban jam’iyya ya riga ya yi magana saboda haka za ku iya tuntuɓar sa.”

Rikicin jam’iyyar NNPP a Kano dai ya janyo dakatar da sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol.

Dakatarwar ta zo ne jim kaɗan bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jogoranci sasanci tsakanin sakataren gwamnatin, Abdullahi Bichi da wasu ƴan mazaɓarsa.

Baffa Bichi dai ya nesanta kansa ne daga zargin kafa wata ƙungiya mai suna “Tsaya da Ƙafarka” da ke fafutukar raba kan gwamna Abba Kabir Yusuf da ubangidansa, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *