Babban Bankin Najeriya ya yi ƙarin kuɗin ruwa da kashi 2% karo na biyu kenan cikin wata ɗaya, inda yanzu ya kai kashi 24.75, a cewar gwamnan bankin Olayemi Cardoso.
Shi ne karo na biyu da CBN ya yi ƙarin a cikin wata daya, bayan ƙara kashi 4% a watan Fabrairu.
Shawarar babban bankin wanda shi ne ƙari mafi yawa a cikin kusan shekara biyu, na da nufin taƙaita samun kuɗaɗen jari da rage hauhawar farashi.
Hauhawar farashi a Najeriya yanzu ta kai kashi 31.7%, sanadin tsadar farashin abinci da na makamashi, tashin kuɗin sufuri da kuma taɓarɓarewar tsaro a yankunan da ake samar da abinci.
Kayan abincin sun haɗar da burodi da shinkafa da nama da nono da kayan marmari duka sun ninka farashinsu.
Najeriya mafi girman tattalin arziƙi a Afirka na fuskantar tsattsauran yanayin tattalin arziƙi, lamarin da ya ingiza mutane da dama cikin talauci.
- Kisan Ummita:Kotu Ta Yanke Wa Frank Geng Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya
- Wani Sojan Gona Ya Fada Komar Dakarun Yan Sandan Jahar Kaduna.