Babban hafsan sojin Najeriya ya gargaɗi masu neman a yi juyin mulki

Spread the love

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gargaɗi masu kiraye-kirayen juyin mulki sakamakon matsin rayuwa, inda ya ce haƙuri abu ne mai muhimmanci a mulkin dimokuraɗiyya.

Janar Musa ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da yake ganawa da ƴan jarida a birnin Fatakwal na jihar Ribas, bayan ƙaddamar da ayyukan wasu gine-gine.

Babban hafsan sojin ya buƙaci masu furta irin waɗannan kalamai da su daina.

An dai gudanar da jerin zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a jihohin Kano da Oyo da Ogun a ƙasar ta Najeriya, yayin da mutane ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan masarufi.

Najeriya na fama da hauhawar farashin kayan masarufi da sufuri da kuma ƙarancin kuɗaɗen shiga.

Kotu Ta Umarci Ɗan Baba Impossible Ya Yi Rantsuwa Kan Zargin Dalla Wa Likita Mari

Sojojin Najeriya sun kashe kasurgumin dan fashi a Kaduna

Bugu da ƙari darajar takardar kuɗin naira na ci gaba da zubewa idan aka kwatanta da dalar Amurka, wadda ke da matuƙar tasiri a ɓangaren tattalin arziƙi na ƙasar.

Ana dai ɗora alhakin wahalhalun da al’ummar ta Najeriyar ke fuskanta kan matakin shugaban ƙasar, Bola Tinubu na cire tallafin man fetur a ranar da ya karɓi mulki.

Wannan dai ba sh ne karo na farko ba da sojojin Najeriya ke gargadin ‘yan kasar da ke kiraye-kirayen juyin mulki a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *