Babban hafsan tsaron Najeriya ya kai ziyara Jamhuriyar Nijar

Spread the love

Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya isa birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar a wata ziyarar da ya kai a ƙasar ta yammacin Afirka wadda e ƙarƙashin mulkin Soji.

Babban hafsan soji na Nijar, Janar Mousa Salou Barmo ne ya tarbi tawagar babban hafsan sojin na Najeriya a yau Laraba.

Nijar na daga cikin ƙasashe uku na yankin yammacin nahiyar Afirka waɗanda suka fice daga ƙungiyar Ecowas bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohammed Bazoum.

Ƙungiyar ta Ecowas ta yi ta ƙoƙarin ganin ta dawo da ƙasashen zuwa cikinta, sai dai har yanzu abin ya ci tura.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Bayan ficewar tasu daga Ecowas, Nijar da Mali da Burkina Faso sun kafa wata ƙungiya da suka yi wa laƙabi da Ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel (AES), wato Alliance of Sahel States.

Dukkanin ƙasashen uku na fama da matsaloli na rashin tsaro, inda suke faɗa da ƴan tayar da ƙayar baya masu iƙirarin Jihadi.

Haka nan ƙasashen sun mayar da hankalinsu kan ƙulla alaƙar diflomasiyya da ƙasar Rasha, yayin da suka kwance alaƙar da ke tsakaninsu da ƙasashen Yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *