Babban layin wutar lantarki na kasa a Nijeriya ya sake daukewa gaba daya a yayin da ake kokarin gyara layin da ya kawo wutar zuwa yankin Arewa.
Kamfanin Rararraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya ce wutar ta dauke ne da misalin karfe 2 na ranar Talata.
Da misalin karfe 1 na rana karfin wutar da aka samar a layin shi ne megawat 2,711, amma zuwa karfe biyu karfin wutar ya tsiyaye gaba daya.
Kawo yanzu dai TCN bai bayar da bayan musabbanin daukewar wutar gaba daya ba.
Akalla karo na biyar ke nan da wutar lantarki take daukewa dungurungum a Nijeriya sakamakon lalacewar babban layin wutar na kasa.
Wanann na faruwa ne kasa da mako guda bayan dawo da wutar a jihohi 17 da ka yankin Arewa, bayan sun shafe sama da kwanaki 10 a cikin duhu saboda lalacewar babban layin wutar yankin daga Shiroro zuwa Kaduna.