Babbar kotun jahar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu yan bijilanti 5 kan kashe wani matashi

Spread the love

Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa wasu `yan bijilanti biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta kama su da laifin kisan wani matashi mai shekara 17.

‘Yan bajilantin sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Janairun 2022.

‘Yan bijilantin, waɗanda suke aiki a cibiyar bunƙasa rayuwar matasa ta Sani Abacha da ke kan hanyar Madobi, sun haɗa da Emmanuel Korau da Elisha Ayuba da Irimiya Timothy da Auwalu Jafar da kuma Mustapha Haladu.

Lauyan da ya gabatar da kara Barrister Lamido Soron Dinki, gabannin yanke hukuncin ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake zargi sun kama matashin ne a sabon titi, Panshekara, inda suka far masa da duka da da sanduna, kana daga bisani suka raunata shi ta hanyar caka masa wuka, kana suka ja shi a kasa suka jefa shi cikin keken a daidaita sahu, lamarin da ya yai sanadin mutuwarsa.

Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro

Lauyan waɗanda aka yi ƙarar ya yi ƙokarin kare su, inda ya bayyana cewa sun je ne da nufin kama matashin ba halaka shi ba, bayan an kai musu karan sa.

Sai dai, kamar yadda mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Malam Baba Jibo Ibrahim ya ce, mai shara`a Dije Aboki ta yanke wa `yan bangan hukunci ne bayan ta gamsu da hujjojin da mai gabatar da ƙarar ya gabatar:

Sai dai kuma mutanen da aka yanke wa hukuncin na da damar ɗaukaka ƙara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *