Kotu ta yanke wa wani mai mai garkuwa da mutane hukuncin daursin shekaru 21 a gidan yari a Jihar Kaduna.
Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a GRA Zariya ta yanke wa Mohammed Kyauta Aminu mazaunin kauyen Pan Daudu a Karamar hukumar Igabi hukuncin ne a ranar Litinin.
Daliba Ta Kashe Kanta Saboda Lakcara Ya Daina Son ta.
Kotun ta same shi da laifin mallakar bindiga kirar AK-47 da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma satar shanu.
An dakatar da yin gwanjon kayan Mandela
Da take yanke hukuncin, Mai Shari’a Rabi Salisu Oladoja ta ce kotu ta daure Mohammed ne a karkashin sashi na 45 na Penal Kod 2017 inda zai kwashe shekaru 21 a gidan gyara hali.