Babbar kotun jihar Kano dake zamanta a Miller Road ta dage sauraron shari’ar kisan wata matar aure mai suna Ruma Sha’aibu, wadda ake zargin wani matashi mai suna Sha’aibu Abdulkadir da kashe ta, ta hanyar yi mata yankan rago.
Lamarin ya faru ne a unguwar Farawa, karamar hukumar Kumbotso, a cikin watan Afrilu na shekarar nan ta 2025. Jami’an ‘yan sanda ne suka kama Sha’aibu Abdulkadir, inda daga bisani suka gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
An fara gurfanar da wanda ake zargin ne a kotun majistare da ke No-Man’s-Land, kafin a mayar da shari’ar zuwa babbar kotun jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Farida Danbaffa. Sai dai kotun ta dage zaman ne saboda rashin kawo wanda ake zargin daga gidan yarin.
- Yan Sandan Kano Sun Kama Mace Da Yunkurin Fitar Da Motar Sata Kirar Hillux Jamhuriyar Nijar
- An Gurfanar Da Dattijo Da ’Ya’yansa Biyu Bisa Zargin Sayar Da Kayan Maye A Kano
Duk da haka, lauyar gwamnatin jihar Kano kuma mai gabatar da ƙara, Barista Mardiya Alhassan Dawaki, da lauyan wanda ake zargin, Barista Mustapha Idris, duk sun halarci zaman kotun. Daga nan mai shari’ar tace a gabatar da Sha’aibu Abdulkadir a gaban kotun a ranar 23 ga watan Oktoba.
A nasa ɓangaren, mijin marigayiyar, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa yana fatan kotun za ta yi adalci wajen hukunta wanda ake zargi da kisan matar tasa.