Babbar Kotun Tarayya me lamba 3 dake zaman ta a Unguwar Gyadi Gyadi Kano, karkashin jagorancin mai Shari’a Simon Amobeda, ta Umarci Gwamnatin Jahar Kano ta biya Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero naira Miliyan 10, sakamakon ta ke masa hakki da tsoratar da shi.
Tunda farko Aminu Ado ya shigar da karar ne yana rokon Kotu da ta bi masa hakkinsa na Dan’adam da yake zargin an ta ke masa.
Bayan sauraron rokon Kotun, ta yi hukuncin cewa Gwamnantin Jahar Kano ta biya me karar Naira miliyan 10, sannan yana da damar yin yawo a ko ina a Najeria.
Daga bisani Kotun ta bayyana cewa tana da ikon Sauraran Shari’ar da Sarki na 15 ya shigar
Bayan fito wa daga Kotun Lauyan Aminu Ado, Abdurrazak Ahmad, ya shaida wa jaridar idongari.ng, cewar kotun ta yadda lallai gwamnatin jahar Kano, ta keta hurimin da dokar kasa ta ba wa sarki na 15, don a Kama shi har sai da ingantaccen dalili.
Kazalika Lauyan Gwamnatin Jahar Kano Barr Ibrahim Isa Wangida ya bayyana cewa, wannan hukuncin da kotun ta Yi nasara ce a Gare su , domin ba a taba mutuncin sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi ii , ba inda ma su karar suka roki kotun ta cire shi daga gidansa amma kotun baya bayar da dama ba.
Ya Kara da cewa za su sanar da wadanda suke wakilta , idan da akwai yiwuwar daukaka kara.
- Shari’ar Murja Kunya: Kotu Ta Umarci Hisbah Ta Yi Bayanin Dokokinta Masu Kama Da Juna
- Shari’ar Murja Kunya: Kotu Ta Umarci Hisbah Ta Yi Bayanin Dokokinta Masu Kama Da Juna