Mataimakin babban sufeton yan sandan Nijeriya dake kula da shiya ta daya wato Zone One Kano, AIG Garba Ahmed, ya umarci kwamishinonin yan sandan dake karkashin kulawarsa da su tabbatar da cikakken tsaro a lokacin bukukuwan salla da kuma bayan ta.
Kwamishinonin yan sandan da umarnin ya shafa sun hada da na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori da kuma na jihar Jigawa CP Ahmad Tijjani Abdullahi.
Kakakin rundunar yan sandan shiya ta daya Kano, CSP Bashir Muhammad, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.
Sanarwar ta ce , AIG Garba, ya umurci sashen tattara bayanan sirri da su rika bin sahun duk wasu abubuwan da ke faruwa a jihohin biyu don wanzar da zaman lafiya.
Haka zalika ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar bikin Babbar Sallah , da za a gudanar a ranar 10 ga Zulhijja, 1446 Hijira (wanda yayi daidai da 6 ga Yuni, 2025).
- Ya Kamata Najeriya Ta Gina Katanga A Kan Iyakokinta – CG Musa
- Hukumomin Tsaro Sun Haramta Hawan Sallah A Kano
Ya kuma tabbatar da kudurin rundunar wajen samar da isassun tsaron da su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da Jigawa da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin natsuwa da bin doka da oda, inda ya roƙe su da su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’in samun zaman lafiya,
A ƙarshe, AIG Ahmed ya bukaci a ci gaba da basu hadin kai da kuma basu bayanan da za su taimakawa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu