Babu gaskiya kan cewa ƴan Najeriya na fuskantar barazana a Afirka ta Kudu

Spread the love

Sashen kula da hulɗa da ƙasashen ƙetare na ƙasar Afrika ta Kudu ya bayyana takaci kan sanarwar da ofishin jakadancin Najerya a Pretoria ya fitar, yana shawartar ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasar su yi taka tsantsan a lokacin karawar da za a yi tsakanin Najeriya da Afirka ta kudu a gasar Afcon da ke gudana a Ivory Coast.

Wata sanarwa da mai magana da yawun sashen hukumar kula da huldar kasashen waje a Afrika ta Kudu, Mr Clayson Monyela, ta fitar a yau Talata, ta ce shawarar abun takaici ce, saboda hakan zai iya haifar da tunzuri, a tsakanin yan kasar ta Afika ta kudu da Najeriyar da ‘yan Najeriyar da ke da sha’awar zuwa kasarsu.

‘Muna da yakinin cewar Afirka ta Kudu da ke kaunar wasanni, babu wata barazana ga ‘yan Najeriya, kuma ba mu amince da irin kalaman da ofishin jakandancin Najeriyar ya yi ba’ inji Mr Clayson Monyela.

Osimhen zai buga wasan Najeriya da Afrika ta Kudu

Sanarwar ta kuma bayyana cewar a lokuta daban-daban kungiyar kwallon kafan Afrika ta Kudu Bafana-Bafana ta sha karawa da ta najeirya ta Super Egale, ba a kuma taba samun tarihi na wani rikici ko fada da ke alaka da karawar kasashen biyu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *