Babu hannuna a komawar Aminu Ado zuwa Kano – Ribadu

Spread the love

Ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya musanta zargin hannun Nuhu Ribadu a komawar da Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi zuwa Kano.

Mataimakin gwamnan jihar kano Kwared Aminu Abdussalam ne ya zargi Nuhu Ribadu da kitsa komawar Aminu Ado Bayero zuwa Kano ta hanyar ba shi jami’an tsaro da jirgin sama domin mayar da shi jihar.

”Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ne ya bayar da jirage guda biyu domin ɗauko tsohon sarki domin su kawo shi Kano”, in ji mataimakin gwamnan.

To sai dai kakakin Nuhu Ribadun, Zakari Mijinyawa ya shaida wa BBC cewa babu hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a komawar tsohon sarkin.

”Ba gaskiya ba ne, babu wanda ya bayar da jirgi domin mayar da shi, saboda wannan ba aikinmu ba ne”, in ji Mijinyawa.

Dangane da zargin da mataimakin gwamnan ya yi cewa har da jami’an tsaro ofishin Ribadun ya aika Kano, Zakari ya ce ba haka batun yake ba.

”Babu wani jami’in tsaro da muka tura Kano, ai suma suna da jami’an tsaro, ai kwamishinan ‘yan sandan jihar ya gabatar da taron manema labarai, kuma kowa ya ji yana cewa aikinsa yake yi, ba wanda ya saka shi”.

Ya ce bai kamata a riƙa sanya siyasa a cikin kowane irin batu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *