Rukunin kamfanin Dangote a Najeriya ya ce bai aikata wani laifi, ko ba daidai ba da ya sa jami’an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa suka ziyarci babban ofishinsa ba.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar kan ziyarar da jami’an hukumar suka kai babban ofishinsa da ke Legas ranar 4 ga watan Janairu, ya ce ya fahimci girman damuwa da maganganu da hakan ya janyo tsakanin abokan hulɗarsa, da sauran mutane, don haka ne ma kamfanin ya ce ya fitar da sanarwar don fayyace ainihin abin da ya faru.
Sanarwar ta ce a ranar 6 ga watan Disamban 2023, ya samu wasiƙa daga Babban Bankin ƙasar, CBN, inda aka buƙaci kamfanin ya bayar da bayanan canjin kuɗin ƙasar waje da CBN ɗin ya bai wa kamfanin tun daga shekarar 2014 zuwa yau.
Kamfanin ya ce ya kuma rubuta wa hukumar EFCC takardar da ke nuna cewa kamfanin ya karɓi takardar buƙatar bayar da bayanan da aka buƙata.
”Mun kuma buƙaci ƙarin lokaci domin kammala tattara bayanan, don gabatar da su kamar yadda aka buƙata kasancewa bayanan shekara 10 aka buƙata”, in ji sanarwar.
To amma kamfanin ya ce hukumar EFCC ba ta ba shi amsa kan buƙatar ƙarin lokacin da ya nema ba, sannan bai ƙara musu lokacin ba, a maimakon haka sai ya dage cewa sai kamfanin ya gabatar da takardun bayanan da aka buƙace shi a lokacin da aka buƙata.
Sanarwar ta ƙara da cewa duk da ƙurewar lokacin da ya fuskanta, ya tabbatar wa da hukumar EFCCn aniyarsa na gabatar da takardun amma ya alƙawarta gabatar da takardun rukuni-rukuni.
Kamfanin ya ce a ranar 4 ga watan Janairun 2024, wakilansa suka gabatar da rukunin farko na takardun ga hukumar EFCC, amma sai jami’an na EFCC suka ki karɓar takardun, suka dage cewa sai sun ziyarci babban ofishinsa domin karɓar takardun da hannunsu.
”A yayin da wakilan kamfaninmu ke ofishin EFCC don gabatar da takardun, sai ga jami’an hukumar a ofishinmu da nufin karɓar takardun da an riga an kai musu ofishinsu, sun zo a wani yanayi da ba mu ji daɗinsa ba, domin hakan tamkar wulaƙanta mu ne” kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ”Abin takaicin ma shi ne jami’an ba su karɓi takardun a babban ofishin namu ba lokacin ziyarar tasu, kasancewar tuni takardun na ofishinsu”.
Kamfanin ya ce a matsayinsa na wanda ke bin doka da oda, a kodayaushe a shirye yake ya baiwa hukumar ta EFCC haɗin kai bisa duka bayanan da take nema.
”Tuni mun bai wa hukumar rukunin farko na takardun da take buƙata, kuma muna aiki wajen tattara rukuni na biyu domin bai wa hukumar a kan lokaci domin gudanar da aikinta”.
Kamfanin na Dangote ya ce – a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu taimaka wa tattalin arzikin Najeriya, kuma babban kamfanin da ya fi ɗaukar ‘yan Najeriya aiki, wanda kuma ya kasance ɗaya daga cikin mayan masu biyan haraji a ƙasar – a kodayaushe shi mai bin doka da oda ne, kuma a shirye yake wajen yin duk wani abu da zai taimaka wajen mayar da ƙasar mai kyakkyawan yanayin zuba jari ga ‘yan ƙasar da na ƙetare.