Babu luwaɗi da maɗigo a yarjejeniyar da muka saka wa hannu – Gwamnatin Najeriya

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da sanya hannu kan Yarjejeniyar Samoa, tana mai cewa ta ƙunshi ayyukan cigaban al’umma ne ba amincewa da auren jinsi ko kuma kare haƙƙin ‘yan luwaɗi ba.

A ranar Laraba ne wasu rahotonni suka ambato cewa gwamnatin tarayya ta saka hannu kan yarjejeniyar, wadda ta ƙunshi wasu alƙawurra tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai, da gamayyar ƙasashen yankin Karebiya da na Pacific .

Rahotonnin sun ambato cewa baya ga ayyukan raya ƙasa da cigaban al’umma, yarjejeniyar ta kuma ƙunshi batun amincewa da gwagwarmyara neman ‘yanci da masu fafutikar luwaɗi da maɗigo ke yi a ƙasashen.

Sai dai cikin wata sanarwa, ma’aikatar yaɗa labarai ta ce Najeriya ta bayyana ƙarara cewa “ba za ta yarda da duk tanadin da ya saɓa wa dokar Najeriya ba” kafin ta saka hannu.

“Ya zama wajibi mu tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin Bola Tinubu… ba za ta saka hannu kan wata yarjejeniya ba da za ta ci karo da muradan mutanenta ba,” a cewar Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris cikin wata sanarwa a yammacin yau Alhamis.

“Kafin amincewa da yarjejeniyar, wakilanmu sai da suka tsefe duka alƙawuran da aka yi tsakanin Tarayyar Turai da ƙasashen OACPS.

“Yarjejeniyar ba wani abu ba ce illa tsarin shari’a da zai ba da damar haɗin gwiwa tsakanin OACPS da Tarayyar Turai domin cigaban al’umma, da daƙile sauyin yanayi, da samar da kuɗaɗen zuba jari.”

A shekarar 2014 Najeriya ta amince da dokar haramta alaƙar aure tsakanin jinsi ɗaya, abin da ke nufin luwaɗi da maɗigo haramtattu ne a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *