Babu wanda muka wanke kan binciken hukumar jinƙai – EFCC

Spread the love

A Najeriya, Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta musanta rahotanin da ke cewar ta wanke wasu mutane da ake zargin suna da hannu a almundahanar da ake zargin an tafka a ma’aikatar kula da jinƙan al’ummar ƙasar da ta yi sanadiyar dakatar da Betta Edu daga ministar ma’aikatar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ya fitar a jiya Lahadi ta ce har

hukumar tasu ta EFCC na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Sanarwar ta ce babu wani jam’i daga ma’aikatar kula da jinƙan Najeriya da aka gayyata don amsa bayanai a hukumar ko ita kan ta dakatacciyar ministan ma’aikatar Betta Edu,”Bamu wanke kowa daga almundahanar da ake zargin an tafka a ma’aikatar.

Sanarwar ta EFCC ɗin ta ce kawo yanzu ta yi nasarar karɓo naira biliyan 32.7 da dala dubu ɗari 445 daga ma’aikatar.

Haka kuma ta ce kuɗaɗen da ta iya ƙarbowa na daga cikin kudaden da aka yi almundahanarsu daga cikin kudaden da tallafin korona, da na bashin bankin duniya, da kudaɗen Abacha da aka karbo, dukkansu aka baiwa ma’aikatar kula da jinƙan al’ummar ƙasar.

Sai dai a sanarwar ba ta ambaci sunan ko da mutum guda ba, da ta ke zargin na yaɗa wasu bayanai ba, sai dai hukumar ta ce suna mayar da martani ne akan wasu bayanai da ake yaɗawa na cewar hukumar ta wanke wasu daga cikin wadanda suke bincika.

Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar ta EFCC a wata mujallar hukumar ta EFCC da mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ya aikewa da BBC a ƙarshen watan Maris ɗin nan, ta na mai ambato shugaban hukumar Ola Olukoyede, sun yi nasarar karɓo naira biliyan 30, sannan suna bin ciken wasu bankuna 50.

A ranar Litinin 8 ga watan Janairun shekarar da muke ciki ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ministan jinƙan al’ummar ƙasar Betta Edu bi sa zargin tafka jerin almundahana da ya janyo ce-ce-ce-ku-ce.

Taƙaddama ta kunno kai ne sakamakon zargin da aka yi wa Betta Edun na bayar da umarnin a biyan sama da naira miliyan 585 cikin asusun ajiyar wata mata, lamarin da ya saɓa da ƙa’idar aiki.

Haka kuma ana zarginta da keta dokokin tafiyar da dukiyar al’umma, ciki har da amincewa da biyan kuɗin tikitin jirgin sama zuwa jihar Kogi.

Haka zalika, an zarge ta da biyan kuɗin shiga taksi daga filin jirgin sama zuwa cikin gari ga ma’aikatanta a lokacin wata ziyara, don kai tallafin dogaro da kai ga wasu masu rauni a jihar.

Waɗanda suka bankaɗo zargin sun yi ta kafa hujja ta hanyar wasu takardun biyan kuɗi da suka yi zargin ministar ta amince da su a shafukan sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *