Babu wata gwamnatin da za ta yi nasara ba tare da yan jarida ba: Hajia Sa’adatu Mustapha Kaltungo.

Spread the love

Shugabar kwamitin bikin raya al’adu ta masarautar Kaltungo a jahar Gombe, Hajia Sa’adatu Mustapha ( Alkyabbar Kaltingo) ta bayyana yan jarida a matsayin masu bayar da gudunmawa, ta fuskar wayar da kan al’umma da sauran fannonin ci gaba.

Hajia Sa’adatu Mustapha , ta bayyana hakan ne , a wajen liyafar cin abincin dare da mai martaba Mai Kaltungo, Engineer Saleh Umar O.O.N. ya shirya yan jaridu a fadarsa domin karrama su.

idongari.ng ya ruwaito cewa, Ana gudanar da bikin raya al’adun ne duk shekara a masarautar Kaltungo dake jahar Gombe, inda ake bayyana abubuwan al’ada daban-daban na al’ummar masarautar da ma makotansu.

Alkyabbar Kaltungo ta yi kira ga yan jaridu da su rika gudanar da aiyukansu ba tare da jin tsoro ko jin shakkun tsage gaskiya komai dacinta ba.

Ta kara da cewa babu wata gwamnati ko mai mulki da zai cimma nasarar nanufofinsa ba tare da yan jarida sun yi aikinsu wajen yada burinsa da manufofinsa ba.

Ta gode wa yan jaridar da suka amsa gayyatar mai martaba Mai Kaltungo daga jahohi sama da 11 a fadin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *