Babu yarjejeniyar yin karɓa-karɓa tsakanina da Atiku – Kwankwaso

Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta raɗe-raɗin da ke cewa an cimma yarjejeniya tsakaninsa da tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun hamayyar ƙasar – Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP – kan cewa kowannensu zai yi mulki na wani wa’adi.

A hirarsa da BBC, Kwankwaso ya ce bai san da maganar ba, amma ya samu labarin cewa ɓangaren Atikun na ta “yin taruka da shugabannin yankin ciki har da malamai, suna faɗa masu wannan magana”.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce ”Wannan magana ta ƙona mani rai matuka, a ce dattawa suna ƙarya, suna faɗar abun da ba a yi ba, an faɗa min an tara kusan malamai arba’in da biyar ana gaya masu wannan magana wacce babu ita, ko kaɗan ban ji daɗin wannan abu ba” in ji tsohon dan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP.

Ya kara da cewa ”An gaya musu wai na amince cewa Atiku zai yi shekara hudu, nima zan yi hudu, shi kuma Peter Obi ya yi shekara takwas, wannan maganar babu ita, ba a yi ta ba” in ji Kwankwaso.

Ya ce tun da ya bar PDP ya koma NNPP ya samu nutsuwa, kana ya huta da abun da ya kira ‘Wulakancin da jam’iyyar PDP ta yi masa shi da mutanensa”

”Irin wadannan ƙarairayi, da yaudara ne suka sa muka fice, da ni da shi Peter Obi da Wike, dukkanmu muka tafi, yanzu ga shi sun zo suna ci gaba da yi, kuma mu din nan da aka wulaƙanta aka kore mu, yanzu ake so mu zo mu sa waɗanda suka wulaƙanta mun a gaba domin a samu nasara.

Martanin Kwankwaso kan – (Abba tsaya da ƙafarka)

Tsohon gwamnan na Kano Sanata Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda wasu ke neman haifar da ɓaraka tsakaninsa da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, biyo bayan wata sara da aka fito da ita a baya bayan nan mai taken (Abba Tsaya Da Ƙafarka), wadda ke neman gwamnan ya yi wa mai gidan na sa bar’a, ya raba gari da shi, saboda zargin ya kankane al’amuran gwamnati, ya hana ruwa gudu.

”Abun da mutane ba su gane ba shi ne mu fa Kwankwasiyya ƙungiya ce ba jama’iyya ba, mutane ne suka amince da mu, don haka idan gwamna ko wani dan majalisa da muka saka ya zo yana abun da ba shi ake so ba, ba wai sunansa kaɗai za a faɗa ba, cewa za a yi Kwankwasiyya ta gaza” in ji Kwankwaso.

Ya ce babu ƙanshin gaskiya a zargin da ake yi masa na cewa yana shiga sharafin gwamnati har ya ce ga yadda za a yi, inda ya ce tun farko ya ce zai rika bayar da shawara ne idan an nema, kuma abun da yake yi yanzu ma kenan, kuma shawarar ma sai an nema.

A cewar Kwankwaso, masu neman Abba ya tsaya da kafarsa, mutane da ke da wata manufa ta siyasa, da suke ganin idan sun raba su, za su samu wata kofa da za su cimma manufarsu.

‘Wasu itunannun gani suke idan ya tsaya da ƙafarsa ya bar Kwankwasiyya, ba mamaki akwai masu neman gwamna a cikinsu, so suke idan ya yi kuskure sai su hada da mu da shi gaba daya su cimma manufarsu, don haka ina so in godewa shi gwamna, dama da shi suke, to ya fito ya ce ahir” in ji Kwankwaso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *