Wani Masanin Tsaro Ya Bayyana Hanyoyin Da Za A Bi Wajen Magance Fadan Daba.

Spread the love

Nazifi Bala Dukawa

Wani masanin tsaron da Ma’adanai Alhaji Baba Habu Mika’ilu Warure ya yi kira ga matasa da su rungumi zaman lafiya da sana’oin doga da kai domin samun rayuwa ingantacciya.

Baba Habu Warure, ya bayyana hakanne jaridar idongari.ng, a ranar Lahadi, a wata gana wa ta musamman a birnin kano.

Warure ya ce babu wani amfani da rayuwa mara kyau , da  zata yi wa matashi fa ce yin da na sani anan gaba,

Ya kara da cewa akwai bukatar gwamnati da sauran Mawadata da su sama wa matasa sana’oin dogaro da kai don tsame su , daga shiga aiyukan daba da kwacen wayoyi da afkawa dukiyoyin al’umma.

Masanin tsaron ya ce wajibi ne a yabawa kokarin yan sanda jihar Kano wajan cafke  mutane 22 da ake zargin sun addabi Dorayi, tare da fattataki yan daban da suka addabi yankin da sauran unguwani da ake fama da fadan daban a jahar.

An yi wa kamfanin sadarwa na AT&T na Amurka kutse cikin bayanan kwastomominsa

Sabon Rikicin Siyasa Ya Kunno Kai Tsakanin Gwamna Uba Sani Da Nasir El-Rufa’i.

Baba Habu, ya ce akwai bukatar a dage da addu’a a dai dai wannan  goman karshen azumin watan Ramadan domin Neman daukin Allah kan hallin da Nigeria ta ke ciki, inda ya yi kira ga yan vigilante da su taimaka  al’ummar musulmi lokacin Tafiya sallah dare don ba su kariya.

A karshe ya yi kira ga mawadata da sauran kungiyoyin da daidai Kun mutane da su duba halin da marayu suke cikin wajan share mu su hawaye da ba su kayan sallah da abinchi domin cire su daga cikin kuncin rayuwa.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *