Bajakoli: KACCIMA Ta Kudiri Aniyar Daukar Matakan Yadda Za A Dinga Kai Kayan Da Aka Sarrafa A Gida Zuwa Ketare.

Spread the love

Cibiyar kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da Noma ta jahar Kano, KACCIMA, ta bayyana kyakkyawan shirin ta, kan yadda za a gudanar da Bajakolin kayayyaki na shekarar 2204 a jahar.

A cewar cibiyar ta kudiri aniyar daukar matakan yadda za a dinga kai kayan da aka sarrafa a gida zuwa kasashen ketare, duk da cewa Dalar Amurika ta yi tashin gwauro zabi, saboda yawan bukatar da mutane ke yi na siyan kayayyaki daga kasashen ketare.

Shugaban Cibiyar KACCIMA, Malam Garba Imam, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a gudanar a ranar Talata.

Ya kara da cewa, yan Nigeria sun saba shigo da abubuwa wanda hakan yake kara neman Dala, amma da za a dinga siyan kayan da ake sarrafawa a gida zai kawo sauki.

Malam Garba Imam, ya kara da cewa Kamfononin da wadanda za su zo yin bajakolin kayayyakinsu a wannan shekarar 2024 sun haura 300 kuma kudin. shiga kyauta ne ga yan kallo.

Haka zalika cibiyar za ta bayar da PASSWORD na Data , tun daga bakin kofa, don samun damar gudanar da bincike ga mahalatta bajakolin ba tare da mutum ya biya kudi ba.

KACCIMA  ta ce, ta samar da jami’an tsaro isassu da kuma na’urar CCTV don taimaka mu su wajen tabbatar da tsaro, don ganin dukkanin abubuwan da suke faruwa a filin bajakolin.

Daga cikin manyan bakin da za su halacci bikin bajakolin na shekarar 2024, sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Sanatoci da Yan majalissun tarayya da kuma manyan kasuwa ciki da wajen Nigeria.

Za a farar gudanar da bajakolin ne daga ranar 23 ga watan Nuwamban zuwa 7 ga watan Disamba 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *