Bama-baman Lakurawa Ne Suka Kashe Mutane A Silame Ba Harin Sojoji Ba – Sojoji.

Spread the love

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce bama-baman da Lakurawa suka ajiye a ƙauyukan da sojojin suka kai wa hari ne suka kashe mutanen gari, ba hare-haren da sojojin suka ƙaddamar ba.

A ranar Laraba da safe ne aka samu rahotonnin hare-haren jiragen sojin Najeriya a wasu ƙauyuka biyu da ke yankin ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto.

Gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ce sojojin ƙasar ne suka kai harin bisa kuskure, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 10, wani abu da gwamnan ya danganta da ƙaddara.

To sai dai cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta, Manjo JanarEdwar Buba ya fitar ya ce ba harin sojojin ne ya kashe mutanen ba.

Ya ce kafin kai harin, sai da sojojin suka ɗauki tsawon lokaci suna gudanar da cikakken bincike ta hanyar tattara bayanan sirri, sanna suka tabbatar da cewa Lakurawa ne ke karakainarsu a yankin.

”Sannan jirginmu ya ƙaddamar da hare-hare kan wuraren da muka tabbatar da cewa na Lakurawa ne da misalin ƙarfe 6:00 na asubahin ranar 25 ga watan Disamba, ta hanyar amfani da ƙananan makamai domin taƙaita ɓarnar da hare-haren za su haifar,” in ji Manjo Janar Edwar Buba.

Ya ƙara da cewa bayan harin dakarunsu da ke ƙasa sun je wurin domin tantance harin.

”Kuma sun tabbatar mana cewa hare-haren sun yi nasara, domin sun lalata maɓoyar Lakurawan, tare da ‘yar ƙaramar ɓarna a ƙauyen. Haka kuma sojojinmu na ƙasa sun zanta da mutanen ƙauyen inda suka tabbatar musu cewa akwai Lakurawa a inda aka kai harin,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa hare-harenmu sun yi nasara wajen kashe Lakurawa a yankin tare da lalata muhimman abubuwan da Lakurawan ke amfani da su ciki har da makamansu.

”Don haka faɗawar harin kan rumbun makaman Lakuwarar ya haifar da wasu ƙarin fashe-fashen bom a wurare daban-daban, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 10, kuma muna kan bincike domin tabbatar da cewa ko suna cikin masu taimaka wa Lakurawan ko akasin haka,” a cewar sojojin na Najeriya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen yankin sun tabbatar musu cewa Lakurawa na gudanar da harkokinsu a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *