Ban ci bashin ko sisi ba – Gwamnan Sokoto

Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu ya musanta bayanan dake kunshe a cikin rahoton hukumar kula da basussuka ta Najeriya cewa gwamnatinsa ta ƙarɓi bashin kimanin naira biliyan 89 a cikin gida da kuma kusan dala miliyan talatin da bakwai daga waje.

Gwamnan ya ce bai ci bashin ko sisin kwabo ba a cikin wata goman da ya yi yana gwamna, “Ko tsakanin mutum da mutum za a ƙarbi bashi akwai yarjejeniya balle bashin da ya shafi gwamnati, kuma ana bin dokar zuwa majalisa kafin a anso bashin amman mu ba mu yi ko wanne ba.”

Alhaji Ahmed Aliyu ya ce rahoton ƙarya ne bai da asali bai da tasiri, kuma yana kira ga dukkan wanda ya ce ya ci bashi ya zo ya bada shaidar hakan,” Idan ma an yi domin a ɓata mani suna ne, hakan bai shiga ba saboda a matsayina na gwamnan jihar Sokoto tun lokacin da na anshi mulki ina biyan albashi 18 ko 19 ko 20 ga wata.”

Gwamnan ya bayyana cewa ba wai yana nufin ba zai ci bashi a nan gaba ba, amman dai a halin da ake ciki bai ci bashi ba, kuma babu wani dan kwangila da ke binsu bashi.

Alhaji Ahmed Aliyu ya shaida wa BBC cewa zai dauki mataki kan rahoton da aka yi masa ƙazafi. “Abin da muke samu da shi muke amfani muna yin abubuwan da suka kamata.

A makon da ya gabata ne dai hukumar kula da basussuka ta Najeriya ta fitar da rahoton bayanan basussukan da gwamnonin suka ci a cikin wata shida, inda rahoton ya ce sababbin gwamnonin jihohi 13 na ƙasar ciki har da Kano, da Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna sun ci bashin naira biliyan 226 daga masu bayar da bashi a ciki da wajen ƙasar.

Gwamnonin jihohin na daga cikin gwamnoni 16 na ƙasar da suka ci bashin bayan rantsar da su a kan mulki a cikin watan Mayun 2023, inda hukumar kula da basukan ƙasar ta ce ta haɗa alƙaluman ne bayan jumlar lissafin da suka yi kan farashin dala a kan naira 889.

Rahoton ya ce gwamnan jihar Sokoto ya ciyo bashin dala miliyan 125.1 daga waje.

A shekarar 2023 gwamnonin Najeriya sun sami kason rabon arzikin kasa da ya fi kowanne yawa da ya ɗara na shekara 7.

Wanda ƙaruwar rabon arzikin na ƙasa ga sassan mulkin ƙasar uku, ya faru ne biyo bayan cire tallafin man fetur ɗin ƙasar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi.

Wani ƙwarya-ƙwaryan nazari ya nuna cewar a 2023 gwamnoni sun sami kason rabon arzikin kasa mai yawa da ya kai naira biliya 627 a cikin watan Satumbar bara, sai watan Disamba da suka sami naira biliyan 610, sai Agusta da suka sami naira biliyan 555, sai Nuwamba da suka sami naira biliyan 533, yayin da a watan Yulin 2023 din suka sami naira biliyan 514, sai watan Oktoba 497.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *