Ban samu wasikar cewa masu zanga-zanga za su yi amfani da Eagle Square ba – Wike

Spread the love

Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike ya ce har yanzu bai samu wasika kan buƙatar amfani da dandalin Eagle Square ba domin yin zanga-zanga da aka shirya fara wa ranar 1 ga watan Agusta.

Wike ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a babban birnin tarayya ranar Asabar, gabanin fara zanga-zangar wadda aka yi wa lakabi da “Kawo karshen rashin kyakkyawar shugabanci”.

Ya ce babu wata wasika da aka aika wa ofishinsa na buƙatar amfani da dandalin na Eagle.

Ministan ya ce masu niyyar yin zanga-zanga kada su yi amfani da kafafen sada zumunta kawai wajen aika sako zuwa ofishinsa. Ya ba su shawarar cewa su bi hanyoyi da suka kamata wajen yin hakan.

Tun da farko, Wike ya yi gargaɗi kan yin zanga-zangar.

“Ga waɗanda ke son yin zanga-zanga ranar 1 ga watan Agusta, babu wurin yin hakan a babban birnin tarayya,” in ji shi.

Ya kuma gargaɗi masu shirya zanga-zangar da su guji yin hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *