Ba Na Fargabar Tinubu Zai Sauya Ni – Musawa

Spread the love

Ministar fasaha da raya al’adu ta Najeriya, Hannatu Musawa ta ce ba ta damu da batun shirin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ke yi ba na yin garambawul a majalisar zartarwarsa.

Ministar ta bayyana haka ne a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi.

An tambayi ministar cewa ko tana fargabar shugaba Tinubu zai iya cire ta idan aka la’akari da ce-ce-ku-cen da ya mamaye ta bayan ba ta muƙamin minista? sai ta ce ” Bana tunanin akwai wani ce-ce-ku-ce da ya dabai-baye naɗina da kuma ofishina. Abin da zani ce shine, na yi wa shugaba Tinubu kamfen domin ya zama shugaban ƙasa, saboda haka na amince da duk matakin da zai ɗauka.

“Ban damu ba saboda na san cewa ci gaban ƙasa ne a gaban shugaba Bola Ahmed Tinubu, don haka duk matakin da zai ɗauka wajen yin garambawul a gwamnatinsa zai zama mai amfani ga ƴan Najeriya.

An daɗe ana kiraye-kiraye ga shugaban Najeriya da ya sauya wasu daga cikin ministocinsa saboda ana ganin ba su yin abin da ya dace.

A ƙarshen watan da ya gabata, mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya ce shugaban ya bayyana kudurinsa na yin garambawul ga majalisar zartarwarsa, sai dai ba a bayyana lokaci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *