Bankin Duniya Ya Baiwa Najeriya Dala Biliyan 1.5 Bayan Janye Tallafin Man Fetur

Spread the love

Bankin Duniya ya danƙa wa Najeriya bashin dala biliyan ɗaya da rabi bayan gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar da wasu daga cikin tsare-tsaren tattalin arziki, kamar yadda rahoton Channels TV ya bayyana.

Matakin na zuwa ne bayan bankin ya amince da bai wa Najeriyar bashi kashi biyu na jimillar dala biliyan 1.5 kan gyaran tattalin arziki (Reforms for Economic Stabilization to Enable Transformation) da kuma dala miliyan 750 domin ayyukan cigaba (Development Policy Financing Program).

Daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin ta aiwatar akwai cire tallafin man fetur, da kuma bijiro da sabuwar dokar gyaran haraji da ke gaban majalisar dokoki.

An raba bashin ne gida biyu zuwa miliyan 750 kowanne, inda tun ranar 2 ga watan Yulin 2024 aka bai wa gwamnatin Najeriya kason farko, kamar yadda wani ƙunshin takardu da bankin ya fitar ya nuna.

Amma kuma sai a watan Nuwamba aka ba ta kaso na biyun saboda sharuɗɗan bayar da shi na ɗamfare da aiwatar da tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnatin ta Bola Tinubu ke yi a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *