Bankin GT Ya Roki Kotu Ta Cire shi A Karar Da Aka Shigar Da Wasu Bankuna Don Hana Su Rike Kudaden Kananan Hukumomin Kano

Spread the love

Babbar kotun jahar Kano, dake zaman ta a unguwar Miller Road, karkashin jagorancin Justice Ibrahim Musa Muhammad, ta saurari dukkanin rokon dake gaban ta, kan karar da shugabancin kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Kano, NULGE, ta shigar don hana wasu bankuna da kuma hukumar raba arzikin kasa rike kudaden kananan hukumomin Kano 44.

Lauyan masu kara Barista Bashir Yusuf Muhammed Tudun Wuzirci, ya bayyana cewa daman kotun ta ba wa kowanne bangare damar shiryawa kan dukkanin Neman dake gaban kotun.

Ma su karar sun roki Kotun, ta bayar da umarnin Hana CBN da babban akanta na kasa da kuma hukumar raba arzikin kasa rike kudaden kananan hukumomin Kano.

Ya ce sun Bayyana wa kotun dalilinsu kan karar da suka shigar kamar yadda www.idongari.ng, ta ruwaito.

Anasa bangaren lauyan kananan hukumomin, Barista Shamsu Ubale Jibrin, ya ce masu karar sun gabatar da hujjojinsu , kuma basa suka kan rokon domin daman sun shigar da karar ce don Kananan hukumomin su ci gaba da karbar kudaden su kamar yadda doka da kundin tsarin mulkin Nigeria suka bayar, don Bankunan su sakarwa Kananan hukumomin kudaden.

Sai dai lauyan Bankin GT, ya roki Kotun ta cire su daga cikin Shari’ar, domin basa cikin Bankunan da suke bawa kananan hukumomin kudaden su.

Alkalin kotun justice Ibrahim Musa Muhammed, ya bayyana cewa zai sanar da ranar yanke hukunci ga dukkan bangarorin Shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *