Baturiya Mai Shekara 62 Ta Yi Saukar Al-Qur’ani A Kano

Spread the love

Wata baturiya, ‘yar ƙasar Bulgaria, Liliana Mohammed ta yi saukar Alqur’ani mai girma a Jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa aure ne ya kawo Liliana, mai shekaru 62 da haihuwa, zuwa garin Kano sama da shekaru 30, bayan da ta auri wani ɗan kasuwa ɗan jihar, Marigayi Alhaji Ibrahim Sambo.

Da ta ke zanta wa da manema labarai, Liliana ta ce ta musulunta ne shakaru goma da suka gabata, inda daga nan ta fara koyon karatun Alqur’ani.

A cewar ta, ta fara koya ne a gida, duba da shekarunta, a ƙarƙashin wata Malama mai suna Malama Hafsa.

Kamar wasa, a cewar ta, sai gashi ta yi bikin sauka a ranar Asabar a wata makaranta mai suna Mamba’irrahman Islamic School a cikin birnin Kanon Dabo.

“Na ji daɗi da na karɓi Addinin Musulunci. Ina samun farin ciki da kwanciyar hankali. Sannan saukar Alqur’ani ɗin nan ma ta bani farin ciki.”

“Alqur’ani littafi ne mai daɗi kuma shine ya ke zame min jagora a rayuwa ta a halin yanzu. Zan ci gaba da ƙoƙarin yin hadda, duk da cewa dai na tsufa,” in ji Liliana, mai ‘ya’ya biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *