Bauchi: Wata Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Mutumin Da Ake Zargi Da Wallafa Hotunansa Da Mata A Facebook

Spread the love

Wata kotun majistire Mai namba 5, dake zaman ta a jahar Bauchi, ta bayar da umarnin tsare dattijonnan da Ake Zargi da wallafa hotunan wasu mata, a shafin sa na Facebook Yana rungume da su.

Tunda farko jami’an hukumar Hisbah na jahar Bauchi ne suka kama shi, bayan an shigar da korafi akansa don kaddamar da bincike.

A wallafar da mutumin ya Yi abaya , ya nuna cewa ya Yi Lalata da su, Amma matan sunce batun ba haka yake ba, Inda wasu matan suka rasa aurensu wasu kuma suka shiga rudani.

Rundunar Yan Sandan jahar Bauchi, ce ta Gurfanar da shi, agaban kotun bisa jagorancin Mai Shari’a Laraba Hamisu.

An karanto masa kunshin Zargin da Ake Yi masa, Inda kotun ta dage ci gaba da sauraren Shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamban 2024 don Jin ra’ayinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *