Bayan Daukar Matakin Bude Ofishin Yaki Da Ma Su Fashi Da Makami Da Yan Daba, Rundunar Yan Sandan Kano, Ta Fitar Da Hotunan Wasu Daga Aka Cafke A Dorayi.

Spread the love

Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta walllafa hotunan wasu daga cikin Matasan da ake zargi da aikata laifukan fashi da makami a yankin Unguwar Dorayi dake jahar.

Kakkain rundunar Yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana wa hakan ta cikin Wata sanarwa da ya Rana wa manema labarai a Ranar Alhamis.

Kiyawa ya ce , yanzu Kwamishinan Yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, zai buɗe sabon ofishin yaƙi da fashi da makami da kuma laifukan Daba.

CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana hakan a ziyarar da kai yankin Dorayin domin gana wa da Masu ruwa da tsaki, kan matsalar wasu batagarin Matasa da suka Hana al’umma zaman lafiya.

Gumel ya ce daga ranar Laraba zuwa Alhamis sun kama yan fashi da makami 22, kuma ba za su yi wasa da al’amarin ba wajen gudanar da binciken kwakwaf.

Yanzu haka ya ce suna wasu mutane talatin , da ake zargin suna da hannu a aikata aika-aikar.

Wannan dai na zuwa ne , bayan gungun wasu matasa dauke da muggan makamai wadanda suke Neman Hana mutanen Dorayi zaman lafiya.

Jaridar Idongari.ng, ta wallafa sunayen wadanda rundunar yan sandan ke ma, da suka hada da, Duguja gidan Shanu, Baba Habu, Rigiji Tsamiyar Kuturu, Boris , Amiru Maye Yankifi, Yasari Gidan Gobirawa, Chasa Bakin Labi, Kanabaro Bakin Labi, Audu Magwaya, Nakwata Konannen gidan mai, Musa Kwata , Toti, Dan mafiçhi da kuma Riciever ( Risiba).

Sauran sune , Dan Hajiya Dorayi Sabis, Dantanda Dorayi Bakin Labi, Dan Mallam Dorayi Bakin Labi, Babba Dorayi Bakin Labi, Gundura, Nalutu, Malam Audu Dorayi Karama, Mai Kakari Dorayi Karama, Dini Gurgu, Mani, Alin Magashi , Abban Luwai, Tecno, Nasiru Babo da kuma Ahmed Ozil.

Rundunar ta ke duk Wanda ya San yasan su , ko kuma sunji da su garzayo ofishin Yan sanda domin tantance su, ko an bayar da sunayen su bisa kuskure.

Sai dai Kwamishinan ya ce mutane 30n da suka ambata suna son yin zaman gaggawa da su don samun zaman lafiya a yankin Dorayi.

Ya kuma godewa iyaye, ma su rike da masaratun gargajiya, da shugaban karamar hukumar hukumar Gwale , da kuma shugabancin kwamitin aikin tsaro da al’umma bisa hadin Kai da suke bayarwa akoda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *