Bayan watanni 8 An ci gaba da shari’ar Frank Geng Quarong bisa zargin hallaka tsohuwar budurwarsa Ummita

Spread the love

Babbar kotun jahar Kano mai namba 17 karkashin jagorancin mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta ci gaba da sauraren shari’ar Frank Geng Quarong dan kasar Chaina, da ake zargi da hallaka tsohuwar budurwarsa mai suna Ummulkursum Sani Bahari ( Ummita) a ranar 16 ga watan satumba 2022.

A zaman kotun na yau ranar Laraba,jaridar idongari.ng ta ruwaito cewa, lauyan wanda ake zargi Barista Balarabe Muhammad Dan-Azumi, ya nemi afuwar kotun bisa rashin gabatar da jawabinsa na karshe saboda wasu aiyuka na shari’ar zabe.

Sai dai ya ce, ya sami kudin shari’ar baki daya kuma zai gabatar da jawabin abunda da suka fuskanta a cikin shari’ar nan da kwanaki bakwai masu zuwa.

A baya lauyan Frank Geng , ya bayyana wa kotun cewa, baya musun Frank ya soka wa Ummita wuka, amma ya yi ne bada niya ba.

Sai dai lauyar gwamnatin jahar Kano, Barista A’isha Mahmud , ta bayyana cewa, a zaman da ya gabata an kammala sauraron shaidu , kuma an sanya yau domin lauyan wanda ake tuhuma ya gabatar da jawabin sa na karshe , amma bai gabatar ba , kuma sai ya kawo jawabinsa ne za su gabatar da na su.

Wannan dai ya biyo bayan dogon lolacin da kotun ta dauka bata samu zama ba sakamakon wasu aiyuka da alkalin kotun ya yi , na shari’ar zabe.

Mai shari’ar Justice Sunusi Ado Ma’aji , ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Janairu 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *