Shekara ɗaya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, ƙasar na ci gaba da fuskantar sabbin ƙalubale.
Har yanzu dai hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum da iyalensa na tsare a hannun sojojin da suka yi juin mulki.
Ana kuma nuna damuwa kan cewa za a iya tuhumar Bazoum da laifin cin amanar ƙasa da kuma yiyuwar fuskantar hukuncin kisa.
Moussa Coulibaly, lauyan Bazoum, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin mulkin soji na shirin gurfanar da hambararren shugaban a wata kotu ta musamman da ba ta da ‘yancin kai da kuma nuna son kai.
Idan aka same shi da laifi, Bazoum na iya fuskantar hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga.
Gwamnatin ƙasar ba ta tabbatar da ko musanta wadannan zarge-zargen ba.
Shekara ɗaya bayan juyin mulkin ƙasar karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani, har yanzu ba a san makomar ƙasar ba.
Sojojin sun hau mulki ne da alkawuran magance matsalar rashin tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar. Sai dai masana sun lura cewa duk da waɗannan alƙawuran, an kashe sojoji da dama, kuma rashin tsaro na ci gaba da yin tasiri ga rayuwar fararen hula.