Betta Edu: ACM ta shirya gudanar da zanga-zanga a Kaduna, Abuja muddin Tinubu bai dakatar da Ministan Cikin Gida, Tunji-Ojo ba

Spread the love

Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa Consultative Movement (ACM), ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan ya dakatar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo daga muƙaminsa.

Kodinetan ACM na Ƙasa, Kwamred Bilal Galadima, shi ne ya yi wannan kira ranar Laraba a Kaduna.

Ƙungiyar Arewa ta yi barazanar haɗa kawunan takwarorinta don shirya zanga-zanga a Kaduna da Abuja ta yadda komai zai tsaya cak muddin Shugaba Tinubu ya ƙi dakatar da Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo daga kujerarsa.

Kwamred Galadima ya ce kamata ya yi a dakatar da Tunji-Ojo “saboda wulaƙanta ofishinsa” kuma daidai da tanadin doka.

Ya ce, wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ce zuwa ga Shugaba Tinubu yayin da yake martani ga kwangilar da aka ba wa kamfanin New Planet Project Limited, kamfanin da ake zargin na da nasaba da Tunji-Ojo.

A cewar Galadima, sama da ƙungiyoyi 50 sun nuna sha’awarsu na shiga zanga-zangar wadda aka shirya gudanarwa a ranakun Juma’a da Litinin a Kaduna da Abuja.

Ya ce, Ma’aikatar Jinƙai da Yaƙi da Talauci ƙarƙashin jagorancin Dokta Betta Edu, ta biya kamfanin kuɗi miliyan N438.1 na aikin tuntuɓa da ya yi. Ya ci gaba da cewa, kuɗin bangare ne na Naira biliyan 3 da aka ware don shirin tallafa wa marasa galihu a faɗin ƙasa.

“Ya kamata a lura da cewa, kamfanin wanda aka yi wa rajista a ranar 3 ga Maris, 2009, mai lamba 804833, na da Minista Tunji Ojo da matarsa, Abimbola, a matsayin daraktoci tare da Gbadamasi Clement a matsayin sakataren kamfanin.

“Mun yi amannar cewa abin da Minista Tunji Ojo ya aikata ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma dokar ɗa’a. Sassa na 5 da 6 na Dokar Ɗa’a sun haramta wa jami’an gwamnati shiga rikici da kowane irin kasuwanci in ban da harkar noma,” in ji shi.

Tun da fari wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewar Shugaba Tinubu ya sammaci Tunji-Ojo zuwa Fadar Shugaban Ƙasa kan batun almundahanar da ake zargin an tafka a Ma’aikatar Jinƙai.

An gayyaci Tunji-Ojo ne saboda kwangilar aikin tuntuɓa da kuɗinsa ya kai miliyan N438 da aka bai wa kamfanin New Planet Projects Ltd, kamfanin da shi ma Ministan na da hannu ciki.

Kazalika, an rawaito Tunji-Ojo ya maida martani kan zargin cewar kamfaninsa na New Planet Project Limited, ya samu kwangilar miliyan N438.1 daga hannun dakatacciyar Minista Betta Edu.

Ministan ya bayyana cewa kimanin shekaru 15 da suka shuɗe ne ya kafa kamfanin amma ya yi murabus a matsayin daraktan kamfanin bayan zaɓe a 2019.

Yayin tattaunawar da aka yi da shi, Ministan ya gabatar da takardun bayanai na CAC da ke nuni da ya yi murabus daga kamfanin New Planet Project Limited a matsayin darakta tun shekaru biyar da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *