Shugaba Bola Tinubu ya tattauna da takwaransa na Amurka Joe Biden ta wayar tarho.
Tattaunawar da aka yi a yau Talata, ta ta’allaka ne kan wani ma’aikacin Binance mai suna Tigran Gambarayan da aka kama da laifin halasta kuɗin haram.
Wata sanarwar da fadar White House ta fitar, ta ce shugabannin ƙasashen biyu sun kuma tattatauna kan karfafa hukumomin tsaro da kuma buƙatar sakin ɗaya daga cikin ma’aikacin kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto.
“Shugaba Tinubu ya kuma gode wa Amurka bisa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban musamman ma tsaro a Afrika da kuma Afrika ta yamma baki-ɗaya,” in ji sanarwar.
Shugaba Biden ya tabbatar wa Tinubu cewa haɗin gwiwar ƙasashen za ta ci gaba da wanzuwa saboda makomar duniya ta dogara kan Afrika, don haka tana da muhimmanci.
Sun kuma tattauna kan buƙatar bai wa Afrika kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Biden ya kuma yi amfani da damar wajen jajantawa Najeriya kan afkuwar iftila’in ambaliya da ya faru a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.