Bidiyon Yadda Wasu Matasa Suka Nuna Rashin Goyon Bayan Hakimin Da Aka Tura Mu Su A Kano.

Spread the love

Wasu matasa da suka fusata a karamar hukumar Karaye ta jihar Kano sun kori wakilin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a ranar Alhamis.

Daily Trust ta ruwaito cewar wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, lamarin ya faru ne a lokacin da wakilin sarkin ke kan hanyarsa ta zuwa fadar tare da shugaban karamar hukumar, Wada Nababa Tudun-Kaya.

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Alhaji Ibrahim Abubakar II, tsohon Sarkin Karaye, yana daya daga cikin sarakuna biyar da gwamnatin Kano ta kora.

Shaidan ya ce, “Abin da ya faru shi ne wakilin Sarkin ya shigo gari, shugaban riko ya karbe shi da farko. Don haka, a hanyarsu ta zuwa yin rajistar kasancewarsa, wasu fusatattun matasa sun far musu.

“Kun san har yanzu muna son masarautun mu da aka rusa kuma har yanzu ba mu farfado daga abin da ya faru ba. Abin da ya faru ba tashin hankali ba ne ko kadan amma daya daga cikin gilashin motarsu ya lalace.

“Akwai ofishin ‘yan sanda a gaban fadar Karaye; wanda hakan ya taimaka wajen shawo kan lamarin yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa taron al,umma.”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *