Bola Tinubu Ya Kara Wa Kayedo Egbetokun Wa’adin Shekaru 3

Spread the love

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarawa Babban Sefotun ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, kamar yadda wata majiya daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta bayyana.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito an ƙara wa shugaban ‘yan sandan wa’adin shekara uku ne, ma’ana sai zuwa 2027.

Ta ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ne ya bai wa Babbab Sufeton ‘yan sandan takartar ƙara masa wa’adin a ranar Litinin.

A watan Yulin da ya gabata ne Majalisar Dattijan Najeriya ta yi garambawul ga dokar ‘yan sanda ta 2020 ƙarƙashin sashe na 8, wadda ta ci karo da ƙarawa ma’aikacin gwamnati wa’adin aiki bayan shekara 35 ko kuma bayan kaiwa shekara 60 a raye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *