Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shehu Adamu wanda ya kira kansa da na’ibin masallacin gidan Gyaran Hali na Gwauron Dutse daga Hukumar Shari’a ta Kano

Spread the love

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shehu Adamu wanda ya kira kansa da na’ibin masallacin gidan Gyaran Hali na Gwauron Dutse daga Hukumar Shari’a ta Kano

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu bayan zarge-zargen da kayi akan gidan gyaran hali da tarbiyya na Gwauron Dutse na cewar ana lalata da wasu daurarru a gidan! To alhamdulillah wannan hukumar tayi duk abinda ya dace wajen bincike akan wannan zargin da kayi, mun gayyato limaman wannan gida tun da kace kai na ibinsu ne, sannan mun gayyato Kakakin hukumar shima ya amsa mana tambayoyin mu, sannan bamu yi kasa a guiwa ba wajen hada tawaga ta musamman muka shiga gidan domin kara bincika zargin da kake yi, amma cikin ikon Allah ma bamu sami wani abu kusa da wanda kayi zargi a kai ba.

Bayan wannan ma mun sake bincika rijistar gidan na farkon zamanka da ranar da kace ka fita 29 Afrilu babu mai irin wannan sunan gaskiya, har sell din da ka fada mun shiga mun yi binciken kwakwaf amma babu wannan zargi, shi kansa shugaban wannan gidan shima yace a bayan liman yake zama a masallacin tun da ya zo wannan gidan amma bai sanka ba!

Don haka wannan hukumar Shari’a take gayyatar ka domin kazo kayi mana cikakken bayani akan wannan zargin ta yadda zamu gano wannan zargin naka, domin a gaskiya mu bamu ga komai ba akan wannan maganganun naka, an bamu wayarka mun kira mun kasa samunka, don haka muke bada wannan sako gare shi ko wanda ya sanshi ya sanar da shi yazo hukumar Shari’a ta jihar Kano dake lamba 1, titin Abdullahi Bayero kano

Sa Hannun

Musa Ahmad D/iya (Best Seller)

Mukaddashin Dir Public Enlightiment
Shari’ah Commission kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *