Buhari ba ya bin Tinubu bashin komai – Sule Lamiɗo

Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin jajircaccen mutum, wanda ya iya allonsa da kyau, da ba wanda ya zai fito fili ya bugi ƙirji ya ce shi ya taimaka masa ya samu mulkin Najeriya hatta wanda ya gada Muhammadu Buhari.

Lamiɗo wanda yana daga cikin ƙusoshin jam’iyyar hamayya ta PDP, ya ce Tinubu mutum ne da ya iya ruwa, kuma ya yi nazarin yadda abubuwa kw tafiya a lokacin ya kuma yi amfani da dabarunsa da kyau, ya cimma burinsa.

”Saboda haka ba wani mutum da zai fito fili ya ce shi ne silar cin zaɓen Tinubu, hatta Buhari,” in ji shi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jigon na PDP ya bayyana hakan ne a wata hari da jaridar Nigerian Tribune.

Ya ce: Kafin babban taron jam’iyyar (APC) shi (Tinubu) yana Abeokuta, a jihar Ogun, inda ya bugi ƙirjin cewa lokacinsa ne ya mulki Najeriya. Kuma Buhari, yana nan sangan-sangan yana kallo. Bai so Tinubu. Akwai wanda yake so.”

“Hatta mataimakinsa ma Farfesa Osinbajo bai yarda da shi ba; ya so Ahmed Lawan, ne amma lissafinsa bai yi ba. Ka yi shekara takwas ga Arewa kuma kana son wani ɗan Arewa ya sake wata shekara takwas?! A’a No. Wataƙila dai sai nan gaba, domin akwai abubuwan da ba za ka iya jirkitawa ba, ba dai a Najeriya ba a yau,” in ji Lamiɗo.

Ya ƙara da cewa: “Kana shugaban Najeriya, bayan shekar takwas a ofis , ba shi da ƙwarin gwiwa da ƙarfin halin da zai dasa zaɓinsa.”

DANDALIN KANO FESTIVAL

”Yana wajen babban taron, kuma Tinubun da ba ya so, da bai taɓa tsammanin zai yi nasara ba, ya yi nasara. Sabboda haka Tinubu ya san cewa nasararsa ba daga Buhari take ba, saboda haka ba wani abu da Buhari zai ce ya yi masa.

Haka kuma tsohon gwamna na Jigawa ya ce Tinubu ba shi ne zaɓin ƙungiyar kishin Yarabawa ta Afenifere, ba kuma hatta Obasanjo ma ba ya sonshi, to amma ya zama shugaban ƙasa.

”Duk wasu ƙungiyoyi suna nan, ciki har da gwamnoni, amma ya yi nasara. Ya ƙudiri aniyar murƙushe duk wani abu da ya sha masa gaba, kuma ya murƙushe su.

Ya ce, PDP na aiki tuƙuru don ganin ta yi nasara a zaɓukan 2027 , duk da matsalolin da take fama da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *