Buhari na halartar taron majalisar ƙasa da Tinubu ke jagoranta karo na farko

Spread the love

Taron majalisar magabata ta ƙasa na gudana a ƙarƙashin shugabancin shugaba Bola Tinubu.

Wannan shi ne karon farko da ya kira taron tun bayan hawansa mulki watanni 14 da suka wuce.

Daga cikin masu halartar taron akwai tsoffin shugabannin ƙasar 4 wato Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan da Abdussalam Abubakar da kuma Yakubu Gowon.

Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan dai na halartar taron da kansu, yayin da kuma Abdussalam Abubakar da Yakubu Gowon ke halarta ta na’ura.

Haka ma akwai Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kuma Gwamnoni da dama. Sai kuma tsoffin manyan alkalan kotun kolin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *