Uku daga cikin ƙasashen da sojoji suke jagoranta a yammacin Afrika sun ce za su fice daga ƙungiyar raya tattalin azriƙin yankin ta ECOWAS saboda takunkumin da aka sa musu.
Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sanar da haka ne ta cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka karanta a gidan talabijin, suna cewa ECOWAS ta gaza taimaka musu wajen yaƙi da ta’addanci da kuma matsalar tsaro.
“Bayan shekaru 49, gwarazan al’umar ƙasashen BUrkina Faso da Mali da Nijar sun yi takaicin yadda ECOWAS ta sauka daga kan turbar da aka kafa ta, kamar yadda Kanar Amadou Abdramane, shugaban da ke jagorantar sojin da suka yi juyin mulki a Nijar ya karanta.
Rundunar yan sandan Nijeriya ta cafke wanda ya kashe Nabeeha,
Duk Da Hada Layin Waya Da NIN Garkuwa Da Mutane Na Ci Gaba
ECOWAS ta ƙaƙaba wa ƙasashen uku takunkumai tare da dakatar da su daga daga ƙungiyar, biyo bayan kwace iko da sojoji suka yi a jerin juyin mulkin da suka yi, abin da ya haifar da fargaba ta ɓangaren siyasa a Sahel.