Burkina Faso na zargin Benin da Ivory Coast da yunƙurin haddasa tawaye a ƙasar

Spread the love

Shugaban mulkin soja na Burkina Faso Ibrahim Traore ya zargi maƙwabtansu Ivory Coast da Benin da shirya maƙarƙashiya domin tayar da fitina a ƙasarsa.

“Zan sake faɗa, ba mu da wata matsala da mutanen Ivory Coast, amma muna da matsala da shugabannin da ke mulkin ƙasar,” in ji Traore a jiya Alhamis.

Ya ƙara da cewa Adbijan ce “ke ɗaukar nauyin yunƙurin tayar da fitina” a Burkina Faso. Traore ya kuma yi iƙirarin cewa Faransa ta kafa sansanoni a Benin domin horar da ‘yantawaye.

Ya yi iƙirarin cewa yana da wani “sauti da aka naɗa na wakilan Faransa a Benin da ke gudanar da ayyuka daga sansanin ‘yanta’adda” kuma “suke taimaka musu da magani”.

Wannan ne kalamai mafiya girma da Kyaftin Traore ya yi tun bayan jita-jitar juyin mulki da aka yi a watan da ya gabata, kuma an yaɗa jawabin a kafar talabijin ɗin ƙasar ta RTB TV.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *