CAF ta bai wa Najeriya nasara kan Libya a wasan da ba a fafata ba

Spread the love

 

Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Afrika CAF ta bai wa Najeriya maki uku da ƙwallo uku kan Libya, a wasan da ƙasashen biyu ba su buga ba, bayan da aka zargi jami’an Libya da karkatar da jirgin ‘yan wasan Najeriya zuwa wani filin jirgi a ƙasar.

Tun da farko an tsara karawa tsakanin ƙasashen biyu domin neman gurbin shigar gasar Afirka ta 2025.

A hukuncin da ta sanar a shafinta na Intanet, CAF ta bayyana cewa an sami hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya da laifin karya sashe na 31 na dokokin gasar cin kofin nahiyar Afrika da kuma sashe na 82 da 151 na dokokin CAF.

Haka kuma hukumar ta CAF ta ci tarar hukumar ƙwallon ƙafar Libya dala 50,000.

Hukuncin na CAF na zuwa ne kwanaki kaɗan, bayan shugaban hukumar Patrice Motsepe, ya ce hukumar ta himmatu wajen ganin tabbatar da daidaito a harkar ƙwallon ƙafa a nahiyar.

Matakin ya kawo ƙarshen yunƙurin neman gurbin shiga gasar da Libya ke yi, inda ta ƙare da maki ɗaya kacal a wasanni huɗu, yayin da Najeriya wanda ta zo ta biyu a gasar da ta gabata, ke da maki 10, kuma ta kusa tabbatar da gurbinta a gasar da ake gudanarwa bayan shekara biyu-biyu.

Mene ya faru tsakanin tawagogin biyu?

ranar 14 ga watan Oktoba ne ƴanwasa da jami’an tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles suka tsinci kansu cikin wani yanayi bayan da suka shafe fiye sa’a 16 a filin jirgin sama na Abraq da ke Libya.

Tawagar Super Eagles ta je Libya ne domin buga zagaye na biyu na wasan neman shiga gasar kofin ƙasashen Afirka ta 2025 da za a yi a Morocco.

To sai dai an zargi hukumomin Libya da tilasta jirgin Super Eagles sauka a filin jirgin sama na Abraq, maimakon filin jirgin saman Benghazi da tun asali aka tsara ƴanwasan za su sauka, kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta bayyana.

Hotuna da bidiyo da NFF ta fitar a shafukan sada zumunta a lokacin, sun nuna yadda ƴanwasan na Super Eagles suke zaune dirshan a filin jirgin saman, inda suke ta hira bayan shafe fiye da sa’o’i 12 cikin jirgi daga Najeriya zuwa Libya.

Tawagar ta Super Eagles ta yi zargin da gangan hukumomin Libya suka sauya filin jirgin da ya kamata su sauka, yayin da ita ma hukumar ƙwallon Libya ke cewa sun fuskanci irin wannan matsalar lokacin da suka je Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *