CBN Ya Buƙaci Masu POS Su Yi Rajista Da Gwamnati.

Spread the love

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar da wa’adin ranar 7 ga Yuli, 2024 ga masu POS su kammala rajista da Hukumar rajistar kamfanoni ta ƙasar (CAC).

An bayyana hakan ne lokacin da aka yi wata ganawa tsakanin kamfanonin hada-hadar kuɗi na ƙasar da shugaban hukumar ta rajistar kamfanoni, Hussaini Magaji a Abuja ranar Talata.

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban na CAC ya ce wa’adin watanni biyu na yin rajistar ya yi “daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin babban bankin Najeriya”.

Wata sanarwa da CAC ta fitar kuma ta kara da cewa “An ɗauki matakin ne domin kare masu mu’amala da kamfanonin hada-hadar kuɗi tare kuma da ƙarfafa tattalin arziƙi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *