CBN ya ce ya kammala biyan bashin dalolin Amurka da suka maƙale a hannunsa

Spread the love

Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da cewa ya kammala biyan daukacin kudaden kasashen waje da suka makale a hannunsa wadanda aka tantance halaccinsu.

Bankin ya sanar da hakan jiya Laraba a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa Hakama Sidi Ali.

A cewar mai magana da yawun babban bankin, an tura wa bankunan kasuwanci na kasar Dala biliyan daya da rabi a kwanan nan a zaman kason karshen na biliyoyin dalolin mallakin ‘yan kasuwa da kamfanoni da suka makale a hannunsa saboda karancin dala.

Ta ce aikewa da kudin ya biyo bayan wani aikin tatancewa na kwa-kwaf da wani kamfani mai zaman kansa ya yi, inda aka tabbatar da sai hada-hadar da aka yi da gaske ne aka biya kudin da aka yi ta.

Ta ce kuma nan take an tura duk wata hada-hadar da ake da shakku kanta zuwa ga masu bincike domin sake duba ta.

Yan Sandan Kaduna Sun Kama Mutane 3 Da Ake Zargi Da Satar Wayar Wutar Lantarki.

Shugabannin Majalisar Dattijai na nuna rashin adalci wajen jagoranci

Da farkon dai dala biliyan bakwai ce masu bin bashin suka yi ikrarin sun makale a hannun babban bankin, to amma daga bisani binciken da wannan kamfanin ya yi ya gano cewa babu gaskiya a ikrarin, dala biliya 2 da miliyan 400 daga cikin biliyan bakwai din saboda babu wasu takardun shaidar yin hada-hadarsu.

Bankin ya ce manufar daukar matakin biyan bashin ita ce daidaita kasuwar canjin kudi ta kasar abin da zai taimaka wajen sauko da farashi da kuma ba masu saka-jari kwarin gwiwa.

Bankin na CBN ya kuma sanar da cewa kudaden da ke a asusun ajiya na kasashen waje na kasar sun karu zuwa dala biliyan 34 da miliyan 110, karuwa mafi yawa a cikin watanni takwas.

CBN ya ta’allaka haka ga karuwar turo kudade zuwa kasar da ‘yan Najeriya ke yi daga kasashen waje, da kuma karuwar sayen hajoji na cikin gida da masu saka jari da saka jari daga waje ke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *