Babban Bankin Najeriya ya sayar da dala ɗaya kan N1,450 ga ƴan canji masu lasisi a ƙasar.
Babban Bankin ya sanar da matakin ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Ana ganin matakin zai samar da wadatar dala a Najeriya wanda kuma zai sa farashinta ya sauka kan naira.
Ɗaya daga cikin shugabannin ƴankasuwar ƴancin ya shaida wa BBC cewa a ranar Alhamis an yi cinikin dala kusan 1,630, amma bayan sanar da matakin farashinta ya fara sauka
Babban Bankin CBN, ya buƙaci ƴan canjin su saka kuɗi a bankin domin samun dalar cikin farashin mai sauƙi tare da umartar su sayar da sauƙi a kasuwa.