Cibiyar ci gaban al’umma da wayar da kai, Citizen for Development and Education ( CDE) ta bayyana shirinta na sanya wa yan jaridun jahar Kano Gasa, musamman wadanda cibiyar ta ke aiki da su, don gwada yadda suke gudanar da aiyukansu, tare da samar da masanan da za su tantance wadanda suka yi nasara kafin a basu kyauta mai tsoka.
Babban jami’in CDE, Ambasada Ibrahim Waiya, ne ya bayyana hakan, a ya yin taron karawa juna sani na yini daya, da cibiyar ta shiryawa yan jaridu a jahar Kano.
CDE ta ca ta shirya taron ne domin karfafa alakarsu da yan jarida, a matsayinsu na kungiyoyi masu zaman kansu.
”Daya daga cikin gudunmawar da mu ke ganin za mu iya ba su shi ne, ya za a yi mu dinga shirya mu su horo irin wannan daga lokaci zuwa lokaci domin dada sa su, su fahimci wasu abubuwa sababbi kan yadda za su gudanar da aiyuknasu kuma azaburar da su don su kasance masu hazaka ” Waiya”.
Ya kara da cewa, kullum kiran da suke yi wa yan jarida musamman ma su tasowa, kar su dinga yin tunani irin na kasa, wanda suke fatan su fadada tunaninsu don suma su kasance wakilan kafofin yada labaran da suka shahara, a duniya kamar BBC, CNN, VOA, ALJAZIRA da dai sauransu.
”Irin wadannan muke tunani mugani muma na mu, mugansu a manya-manyan kafafen yada labarai na duniya cewa yanzu munsansu, kuma munsan daga inda suka fara tun daga kasa har zuwa wannan matsayin ” cewar Ambasada Waiya”.
- Wata jiha a Indiya ta haramta cin naman shanu a bainar jama’a
- Mun kashe ƴan ta’adda dubu takwas a Najeriya cikin 2024 – Sojoji
Sai dai ya ce hakan ba za ta samu ba, dole sai sun zabura wajen nemi ilimi don sanin yadda za su bunkasa aiyukansu ta hanyar ilimi da sanin doka da kuma sauran al’amura.
” sannan kuma sai sun zama sun bude kwakwalwarsu wajen tunani, yanzu yadda duniya ta ke duniya ce ta gasa mutane babu wanda zai jira ka, idan kana bacci wani shi ne a tsaye yake wajibi ne yan jarida su nuna hazaka” Waiya”.
A karshe ya bayyana gamsuwarsa kan yadda yan jaridun suka amsa kiransu, don karawa mu su sani kan abinda ya shafi aikinsu.
Saurari karin hasaken da Ambasada Ibrahim Waiya, ya yi wa www.idongari.ng
Dr. Bala Muhammed, malami a tsangayar koyar da aikin jarida, a jami’ar Bayero Kano, na daga cikin wadanda suka bayar da horon.