Chelsea za ta yi wasa da Man City da Real Madrid a Amurka

Spread the love

Kungiyar Chelsea za ta fafatawa da Manchester City da kuma Real Madrid a Amurka a wasannin shirin tunkarar kakar badi ta 2024/25.

Chelsea tana ta 11 a teburin Premier League da maki 39, wadda saura 11 ya rage mata a kakar nan a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Sauran wasan da kungiyar Stamford Bridge za ta kara a Amurka har da gumurzu da Wrexham da Celtic da kuma Club America.

Chelsea mai buga Premier League za ta yi tata burza da Manchester City ranar Asabar 3 ga watan Agusta.

Za kuma ta kece raini da Celtic a college football arens wato a Ohio Stadium a Columbus a birnin Ohio.

Ranar Talata 6 ga watan Agusta, Chelsea za ta fuskanci Real Madrid a Bank of America Stadium, Charlotte a Carolina – filin da ta buga wasa a 2015 da kuma 2022.

Jerin wasannin da Chelsea za ta buga a Amurka

Chelsea da Wrexham – Laraba 24 ga Yuli a Levi Stadium a Santa Clara,

Chelsea da Celtic – Asabar 27 ga Yuli a Notre Dame Stadium, Notre Dame, Indiana.

Chelsea da Club America – Laraba 31 ga Juli a Mercedes-Benz Stadium a Atlanta, Georgia.

Wasan da aka fafata a bayan nan tsakanin Chelsea da Manchester City

Kakar 2023/2024

Premier League Asabar 17 ga watan Fabrairun 2024

  • Man City 1 – 1 Chelsea

Premier League Lahadi 12 ga watan Nuwambar 2023

  • Chelsea 4 – 4 Man City

Chelsea da Real Madrid – Talata 6 ga Agusta a Bank of America Stadium, Charlotte, Aewacin Carolina.

Wasan da Chelsea da Real Madrid suka kara a bayan nan

Champions League Talata 18 ga watan Afirilun 2023

Chelsea 0 – 2 Real Madrid

Champions League Laraba 12 ga watan Afirilun We 2023

Real Madrid 2 – 0 Chelsea

Wasan Chelsea da Man City daya ne daga tsarin gurmurzu tsakanin fitattun kungiyoyin tamaula da aka shirya mai suna 2024 FC Series .

Haka kuma Chelsea da Real Madrid za su kece raini a daya daga gumurzun Soccer Champions Tour da ake yi tsakanin manyan kungiyoyi da ake buga a Amurka.

Filayen da Chelsea za ta buga wasa a Amurka

Filin wasa da ke Ohio mai dumbin tarihi zai bai wa magoya bayan Chelsea damar ganin ‘yan wasa da shirin da take na tunkarar badi – wadda kaka ta biyu kenan da ba za ta buga gasar zakarun Turai ba – a filin ne za ta fafata da Manchester City.

Bank of America Stadium yana daga cikin filin da Chelsea za ta gwada ‘yan kwallon da za ta yi amfani da su a badi – a nan ne za a kece raini tsakanin Chelsea da Real Madrid.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *