China ta yi alƙawarin taimaka wa Najeriya a fannin tsaro da tattalin arziki

Spread the love

Najeriya da China sun amince su ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin makamashi, da tsaro, da harkokin kuɗi, kamar yadda ministocin harkokin wajen ƙasashen suka bayyana yau Alhamis.

Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi na ziyara a Najeriya ne a wani ɓangare na ziyarar aiki a ƙasashen Afirka huɗu domin faɗaɗa tasirin ƙasarsa a nahiyar.

Mista Wang ya ce China za ta duba buƙatar da Najeriya ta gabatar mata ta faɗaɗa yarjejniyar amfani da takardun kuɗin ƙasar na Yan.

A ɓangaren tsaro kuma, Wang ya ce China za ta dinga goya wa Afirka baya kodayaushe a zauren tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

“Za mu yi aiki tare da Afirka wajen inganta tsaro da kuma cim ma zaman lafiya ta hanyar ayyukan more rayuwa,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *