China za ta tsaurara matakan sakin aure

Spread the love

Wani ƙudurin doka a China da zai sauƙaƙa yin aure da kuma tsaurara matakan saki ya janyo ce-ce-kuce a kafafan sada zumuntar ‘yan ƙasar.

Cikin wata tattaunawa wadda sama da mutum miliyan 100 suka kalla a manhajar Welbo, al’ummar ƙasar sun soki ƙudurin dokar inda suka yi kiran da a basu damar su ta yin saki a lokacin da suke so, inda suka bayar da misalin cewa idan har aka hanasu saki to za a rinƙa samun matsalar yin aure cikin aure.

A ƙarkashin ƙudurin dokar, dukkan waɗanda ke son yin aure ba sai sun gabatar da takardar rijistar gidansu ba.

Ga waɗanda ke son yin saki kuwa, akwai buƙatar su jira tsawon kwana 30 kafin a amince.

An gabatar da ƙudurin dokar ne bayan raguwar haihuwa da ake fuskanta a ƙasar, inda ake ganin aure kamar ya zama dole saboda a samu haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *