Cibiyar Al’amuran Tsaro Da Muhimman Bukatu ( Institute Of Security And Strategic Studies) Ta Karrama Amb. Ibrahim Waiya Da Lambar Girmamawa.

Spread the love

 

Cibiyar al’amuran tsaro da muhimman bukutu wato ( Institute Of Security And Strategic Studies), ta karrama shugaban cibiyar ci gaban al’umma da wayar da kai, Ambasada Ibrahim Waiya, da Lambar Yabo ta girmamawa, kan gudunmawar da yake bayar wa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Kano da kuma Nigeria.

Taron karrawar ya gudana ne a jiya Asabar , a dakin taro na Shehu Musa Yar’adua Center dake birnin tarayya Abuja kamar yadda Jaridar idongari.ng, ta ruwaito .

 

Sauran wadanda aka karrama sun hada General Christopher Musa, Hon. Justice Edward Amoako Asente da kuma Maj. Gen. Johnson A. O. Ochoga da daidai sauransu.

Haka zalika Waiya, shi ne shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiya na jahar Kano ( KPC).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *